ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto kakakin kwamitin tsaron Abul Fadle Amuyi yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, a jiya Laraba ne aka kammala zagaye na baya-bayan nan a tattaunawar da ke gudana tsakanin kasar Iran da kuma kasashen 4+1 wato kasashen Faransa, Burtaniya, Rasha da kuma Cana, hade da kasar Jamus. Sannan tare da halattar wakilin kungiyar tarayyar Turai .
Gwamnatin kasar Iran dai ta bayyana cewa ba zata koma kan yarjejeniyar shirin nukliyar kasar wacce aka fgi sani JCPOA ba sai in har Amurka ta dauke dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar danagne da shirin nata a shekara ta 2018.
342/